Mataimakin shugaban kasa ya ce ya kamata shugabannin da aka zaba su ke kokarin ganawa da wadanda suka zabe su akai-akai

0 82

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce ya kamata shugabannin da aka zaba su ke kokarin ganawa da wadanda suka zabe su akai-akai.

Mai magana da yawunsa, Laolu Akande, ya ruwaito mataimakin shugaban kasar yana fadin haka jiya a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin kodinetan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya mai barin gado, Edward Kallon.

Akande ya kuma ruwaito Osinbajo yana cewa ba za a iya watsi da ganawa da masu zabe akai-akai ba domin adalchi da zaman lafiya da tsaro da tsarin zamantakewar al’umma, domin kuwa abubuwa ne masu matukar muhimmanci.

Osinbajo ya kuma yaba da goyon bayan da abokan hadin gwiwa ke bayarwa, musamman a karkashin tsarin Majalisar Dinkin Duniya, wanda Edward Kallon ya jagoranta a tsawon shekaru.

Tun da farko, Edward Kallon ya shaida wa mataimakin shugaban kasa muhimmancin kyakyawar hulda tsakanin jama’a da gwamnatocinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: