Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo yace fatara da talauci da sauran matsalolin dake fuskantar Najeriya zasu ninku idan kasarnan ta rabe gida biyu.

Ya fadi haka a jiya yayin da yake karbar tawagar kungiyar goyon bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Osinbajo, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yace za a shawo kan kalubalen tsaro da dama a kasarnan nan bada dadewa ba, kuma Najeriya za ta kara karfi da girma.

Ya kara da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a koda yaushe yana kasancewa mai juriya da mayar da hankali wajen shawo kan matsalolin kasarnan, farawa daga kan tsaro.

Tunda farko, shugaban kungiyar goyon bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Osinbajo, Usman Ibrahim, ya yabawa jajircewar Osinbajo da shugabancinsa wajen karfafa kasancewar Najeriya kasa daya da kuma cigaban kasar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: