Matakan Kariya Daga COVID-19 A Sauƙaƙe

0 275
  1. Nisantar cunkoson jama’a da aƙalla tsawon mita guda.
  2. A goge wuraren taɓawa da hannu da ruwan kashe ƙwayoyin cuta.
  3. A riƙa wanke hannu aka-akai da ruwa da sabulu, da ruwan sinadarin kashe ƙwayoyin cuta.
  4. A guji taɓa hanci, baki da ido da hannun da ba a da tabbacin kuɓutarsa daga ƙwayoyin cutar.
  5. A tare atishawa ko tari da gwiwar hannu maimaikon tarewa da tafin hannu.

Ka sani cewa idan mai cutar COVID-19 yayi tari ko atishawa da hannunsa sannan kuma ya gaisa da wani da hannun, hakan zai iya yaɗa cutar zuwa ga wanda suka gaisa da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: