Matan Fulani 284 ne zasu amfana da shirin bada rancen awaki na gwamnatin jihar Jigawa

0 82

Matan Fulani 284 ne zasu amfana da shirin bada rancen awaki na gwamnatin jihar Jigawa.

Shugaban kungiyar, Miyetti Allah na jiha, Alhaji Adamu Idris Babura ne ya bayyana hakan a lokacin rabon bashin awakin a garin Gumel.

Yace kowacce bafulatana zata sami rance Dan Akuya da kuma Akuya guda biyu.

Alhaji Adamu Idris Babura ya kara da cewar Fulanin jihar Jigawa sun amfana da tsare tsaren gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa tattalin arziki.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka amfana da rancen awakin su yi cikakken amfani dasu, domin bunkasa tattalin arzikinsu tare da godewa gwamnatin jihar Jigawa bisa nuna damuwarta ga alumomin Fulani.

A jawabansu daban daban a madadin wadanda suka amfana da rancen awakin Malama Asma’u Wada Garki da kuma Malama Habiba Haruna Babura sun yabawa gwamnatin jihar bisa wannan karamci tare da alkawarin yin cikakken amfani da awakin wajen bunkasa tattalin arzikinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: