Mai dakin Gwamnan jihar Kaduna, Asiya El-Rufa’i, tace baza a biya kudin fansa ba ga wadanda suka yi garkuwa da ita ba, muddin aka sace ta.

Da take jawabi ga mahalarta taron bayar da horo kan tsaro da zaman lafiya a Kaduna, mai dakin gwamnan, wacce malamace a jami’ar Baze dake Abuja, tace a shirye take ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane muddin hakan zai kawo zaman lafiya ga kasarnan.

Mai dakin gwamnan tace dole yan Najeriya su koma kasarsu ta baya mai zaman lafiya.

Kuma mata nada rawar da zasu taka wajen cimma hakan.

Da take jawabi akan rikice-rikicen kabilanci da ake samu a wasu sassan jihar, ta gayawa matan da suka fito daga kananan hukumomin Chikun da Kajuru da Jema’a cewa su yi watsi da kare-rayin da yan siyasa masu san zuciya ke yaduwa domin raba kan mutane.

Kafin hakan dai Gwamnan jihar Kaduna ya kafe kan cewa bazai taba shiga tattaunawa da yan fashin daji ba, da masu garkuwa da mutane.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: