Matar shugaban ƙasa Remi Tinubu ta kashe kimanin naira miliyan 701 kan tafiye-tafiyen

0 94

Gwamnatin Tarayya ta kashe kimanin naira miliyan 701 kan tafiye-tafiyen matar shugaban ƙasa Remi Tinubu, zuwa ƙasashen waje biyar cikin watanni uku, in ji wani rahoto da jaridar Saturday Punch ta wallafa.

A shekarar 2023, an ware naira Biliyan 1.5 don sayen motocin ofishin uwargidan shugaban ƙasar, kamar yanda aka tanada a cikin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira tiriliyan 2.1 da majalisar dokoki ta amince dashi.

Sai dai kuma, tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce kasafin naira Biliyan 1.5 na motocin ya shafi fadar shugaban ƙasa gaba ɗaya ne ba wai iya ofishin matar shugaban ƙasa ba.

Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta CACOL ta bayyana cewa kashe irin wandan kuɗaden da kundin tsarin mulki bai amince da shi ba, ba daidai ba ne, kuma ya nuna alamar rashin ƙwarewar ƴan majalisar dokokin kasar.

Cibiyar CACOL ta yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba dayin kira don gyara irin waɗannan lamuran, domin a daina kashe kuɗaɗen al’umma a kan abubuwan da ba su da amfani ga jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: