Matatar Dangote zata fara rarraba man fetur da dizal a duk faɗin kasar nan tun daga ranar 15 ga Agusta, 2025

0 175

Matatar Dangote ta sanar da cewa zata fara rarraba man fetur da dizal a duk faɗin kasar nan tun daga ranar 15 ga Agusta, 2025. Wannan shiri zai baiwa masu sayarwa, da ‘yan kasuwa, da masana’antu da sauran manyan masu amfani damar siyen man kai tsaye daga kamfanin.

Don inganta hanyoyin rarrabawa, Dangote ya ƙaddamar da sabbin tankokin iskar gas (CNG) da kuma gina tashoshin CNG. Wannan tsarin zai rage farashin sufuri da kuma taimakawa wajen rage farashin kayayyaki masu amfani da man fetur. Dangote Refinery ya ce wannan shiri na daga cikin ƙoƙarinsa na taimakawa wajen samar da man fetur mai arha a Nijeriya, wanda zai inganta rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa baki daya .

Leave a Reply