Matsananciyar yunwa da take dabbar duniya na matukar hauhawa saboda fadace-fadace

0 88

Matsananciyar yunwa da take dabbar duniya na matukar hauhawa, saboda fadace-fadace da sauyin yanayi da kuma annobar corona da ta jefa mutane miliyan 720 zuwa milyan 811 cikin yunwa a fadin duniya a shekarar data gabata.

Sanarwar wanda majalissar dinkin duniya ta fitar ta hanyar wasu hukumomin ta a wannan shekarar da muke ciki.

Kazalika sanarwa ta bayyana cewa mutane da dama na fuskantar matsanciyar yunwa da kuma rashin abinci a wannan lokacin fiye da shekarar data wuce.

Cikin wani rahotan hadin gwiwa na kungiyar kula da abinci da harkokin noma, da kuma asusun bunkasa harkokin noma, da asusun kula da kananan yara na majalissar dinkin duniyar, da hukumar bunkasa abinci ta majalissar dinkin duniya da kuma hukumar lafiya ta duniya suka fitar.

Haka kuma rahotan ya nuna cewa, annobar da ke addabar duniya ya haifar da rauni ta hanyar samun wadataccen abinci, wanda hakan ya shafi al’aummar duniya baki daya.

Shugaban hukumar kula da abinci na majalissar dinkin duniya ya bayyana cewa kaso goma na cikin yawan mutane miliyan 720 zuwa milyan 811 na fuskantar samun karancin abinci a shekarar data gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: