Akalla Jami’an Gwamnatin Jihar Borno su biyar ne wanda ke aikin rangadin duba ayyuka ne mayakan kungiyar ISWAP suka yi garkuwa da su a jiya Laraba.

Jami’an dai sun gamu da iftila’in ne yayin da suke duba aikin hanyar Chibok zuwa Damboa, inda aka kwashe su ta karfin tsiya.

Lamarin dai ya faru ne kusa da Wovi, wani kauye da ke Karamar Hukumar Chibok.

Wata majiya daga yankin ta tabbatar wa da Manema Labarai cewa wani daga cikin Jami’an da ma direban motar sun samu nasarar tserewa ba tare da jin rauni ba.

Kazalika, wani babban Jami’i a Gwamnatin Jihar ya tabbatar wa Manema Labarai cewa gaskiya ne, kuma abinda ya faru abin takaici ne matuka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: