Labarai

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin soji a yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna inda suka kashe sojoji 11 tare da raunata wasu 19

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin soji a yankin Falwaya dake Birnin Gwari a jihar Kaduna, inda suka kashe sojoji 11 tare da raunata wasu 19.

Wasu ‘yan kato da gora uku suma sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka ramu raunuka a lokacin harin.

An rawaito cewa yayin fadan na awanni 3 da rabi, wanda aka fara da misalin karfe 4 da rabi na yamma, aka gama da misalin karfe 8 na dare, an kone wasu manyan bindigogin yaki guda 3, bayan an raba sojojin da sansaninsu.

Majiyoyin tsaro sunce wajen da aka kai harin babbar hanya ce da ‘yan ta’adda ke tsallakawa daga jihar Neja zuwa jihar Zamfara.

An bayar da rahoton cewa kayayyakin yakin da aka yi asara sun hada da kananan bindigogi; da babbar bindiga da bindigogi 14 samfurin AK47 da babura 10, da sauransu.

Duk da kasancewar an kara turo da wasu sojoji daga sansanin Gwaska da misalin karfe 9 da kwata na dare, babu tabbacin adadin wadanda aka kashe daga bangaren Boko Haram.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: