Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kashe mutane 10 a garin Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis inda ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da wani Abba Sheti Gawi mai shekaru 40 tare da kashe shi bayan ya je yankin Gangatilo domin saro itace.
Majiyoyi sun ce abokai da ‘yan uwan mamacin sun neme shi a yankin amma ‘yan ta’addan sun yi musu kwanton bauna tare da kashe su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ‘yan ta’addan sun kashe mutane tara.
A cewarsa, an yi wa matasan kwanton bauna ne a lokacin da suka je yankin neman Sheti Gawi, wanda Boko Haram suka yi garkuwa da shi, suka kashe shi.
Ya kara da cewa wata tawaga karkashin jagorancin DPO na yankin, DSP Idris Haruna, ta ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda daga bisani suka sada mamacin ga ‘yan uwansa.