Mazauna garin Sundimina dake karamar hukumar Birnin Kudu suna zargin jami’an hukumar NDLEA da kashe wani matashi a wani samame da suka kai cikin dare

0 92

Mazauna garin Sundimina dake karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa, sun zargi jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kashe Murtala Gambo mai shekaru 25 a wani samame da suka kai cikin dare.

Mazauna garin sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, yayin da tawagar ‘yan sintiri ta NDLEA suka isa garin da tsakar dare suka harbe Murtala Gambo.

Wani da ya shaida lamarin mai suna Musa Danburga ya bayyana cewa jami’an sun harbi Murtala Gambo ne a baya saboda ya kira su da ‘yan fashi.

Kawun mamacin, Salisu Gambo, ya shaida wa manema labarai a jiya cewa, sun kudiri aniyar neman hakkin wanda aka kashe amma ba za su iya ci gaba da shari’a da hukumar ta NDLEA ba saboda ba su da kudi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP Aliyu Tafida ya ce rundunar ‘yansandan ta yanke shawarar bankado al’amuran da suka shafi mutuwar ta Murtala Gambo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: