Manajan Darakta na kamfanin man fetur ta kasa NNPC, Mele Kyari, ya bayar da tabbacin kawo karshen dogayen layukan man da ake yi a gidajen mai a kasar.

Mele Kyari ya bayyana haka ne jiya a Abuja lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan halin da matatun man kasarnan ke ciki.

Ya ce akwai isasshen man fetur a kasarnan da zai biya bukatun ‘yan kasarnan.

Mele Kyari ya ce NNPC na da jimillar lita miliyan dubu 2 da miliyan 800 na man fetur a kasar nan wanda ya isa ya biya bukatun al’ummar kasar nan na kwanaki 47 masu zuwa ba tare da an shigo da wani daga waje ba.

Ya danganta matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan da hutun ranar ma’aikata da kuma hutun Sallah.

Manajan Daraktan ya ce tsaikon ya haifar da firgici da ya jawo gaggauta sayen man yana mai cewa hakan ne ya janyo dogayen layukan a gidajen mai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: