Ministan albarkatun ruwa ya ce Najeriya na bukatar aƙalla Naira tiriliyan shida domin biyan bukatun samar da ruwan sha

0 99

Ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu, ya ce Najeriya na bukatar akalla Naira tiriliyan shida domin biyan bukatun samar da ruwan sha a kasarnan.

Suleiman Adamu ya bayyana haka ne a jiya a taron majalisar dinkin duniya kan albarkatun ruwa karo na 28 da aka gudanar a Abuja.

Ministan ya yi nuni da cewa, manyan kalubalen da ke fuskantar ci gaba mai dorewa a bangaren ruwa sun hada da samar da kudade, rashin gudanar da harkokin ruwa yadda ya kamata, rashin kayan aiki, da sauransu.

Ya ce Bankin Duniya ya bayar da dala miliyan 700 don tallafa wa Najeriya a shirinta na samar da ruwa da tsaftar muhalli don farfado da fannin.

Tun da farko Manajan shirin kula da ruwa da tsaftar mahalli na UNICEF, Oumar Dombouya, ya ce sakamakon bincike na yau da kullum kan yanayin ruwan sha da tsaftar muhalli a shekarar 2019 ya nuna cewa kashi 30 cikin 100 na ‘yan Najeriya, kimanin mutane miliyan 60 ne, ba sa iya samun ruwa mai tsafta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: