Ministan Ilimi na kasar Kenya ya sake nanata dokar haramta dukan daliban makarantu a fadin Kasar

0 65

Ministan Ilimi na Kasar Kenya ya sake nanata dokar haramta Dukan Daliban Makarantu a fadin Kasar.

Ministan Ilimin Mista George Magoha a ziyarar aiki ta kwana daya da ya kai wani Yanki, inda ya samu Malamai suna Dukan Daliban ya ce za’a hukuntar Malaman, kamar yadda Doka ta Tanada.

Ko a kwanakin baya an daki wani Dalibi a wata Makaranta da take Kasar, wanda hakan ne ya sa ya ji raunika a Kodar sa.

Ma’aikatar Ilimin Kasar ta umarci a Kama shugaban Makarantar da Malaman da suka yi Dukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: