Labarai

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa Chris Ngige ya shiga jerin takarar neman kujerar shugaban kasa a tutar jam’iyyar APC

Ministan kwadago da samar da ayyukan yin a kasa Chris Ngige, ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa a tutar jam’iyyar APC.

Ofishin yada labaransa ne suka bayyana hakan a jiya, cewa ministan ya sha tuntubar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sa ta APC da kuma jiga-jigan jam’iyyun siyasa harma da yan adawa kafin ya yanke wannan hukuncin.

Kuma a ranar 19 ga Afrilu zai bayyana aniyar sa a bainar jama’a.

Ya kara da cewa Ngige a lokacin dayake tuntubar jam’iyyun siyasa na adawa a lokacin da yayi jawabi ga magoya bayansa a garin Amansea da ke kan iyaka da jihar Enugu bayan ya ziyarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, anan ma ya tabbatar da cewa zai tsaya takara.

Ngige ya kara da cewa yana da damar kasancewa cikin wannan gwamnati kuma yana cikin majalisar dattawa ta 7.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: