Ministan Lafiya Joe Phaahla yace Mutum na biyu ya mutu daga cutar ƙyandar biri a Afirka ta Kudu

0 100

Ministan Lafiya Joe Phaahla yace Mutum na biyu ya mutu daga cutar ƙyandar biri a Afirka ta Kudu, sa’o’i 24 kacal bayan da kasar ta ba da rahoton mutuwar mutum na farko daga kwayar cutar.

An gwada mutum biyu ɗin da suka mutu waɗanda maza ne ƴan shekaru 37 da 38, inda aka tabbatar da cewa cutar mpox ɗin ne musabbabin mutuwarsu.

Minista Phahla ya bayyana cewa, Afirka ta Kudu ta sami rahoton bullar mpox guda shida a wannan shekara, da suka haɗa da biyu a Gauteng da hudu kuma a KwaZulu-Natal.

Dukkan lamuran cutar sun kasance masu tsanani kuma suna buƙatar asibiti.

Leave a Reply

%d bloggers like this: