Ministan Lafiya, Osagir Ehanire, yace cutar kansar baki na jawo mutuwar mutane 764 kowace shekara a Najeriya.
Ya fadi hakan a Abuja yayin shirin bayar da horo akan kansar baki wanda wata gidauniya ta shirya.
Ministan wanda ya samu wakilcin shugabar sashen kula da lafiyar hakora na ma’aikatar, Dr Gloria Uzoigwe, yace ana samun sabbin mutane Dubu 1 da 146 a Najeriya dake kamuwa da cutar kowace shekara.
Yace cutar kansar baki na cigaba da kasancewa daya daga cikin manyan cutukan kansa dake jawo asarar rayuka a Najeriya saboda rashin kai rahoton cutar a asibitoci da kuma yadda ma’aikatan lafiya ke kasa gano cutar tunda wuri.
Ministan yace gwamnati za ta kaddamar da wani sabon kudiri akan lafiyar baki a watan Nuwamban bana.
Daraktan zartarwar gidauniyar, Seidu Bello, yace fasahar zamani na taimakawa wajen gano cutar kansar baki da wuri da sauran cutukan da suka shafi baki.