Ministan Ma’aikatar Sufuri ta Kasa ya bayyana cewa Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja zai Cigaba da aiki

0 58

Ministan Ma’aikatar Sufuri ta Kasa Mista Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja, zai Cigaba da aikin a yau Asabar.

Idan za’a ita tunawa de gwamnatin tarayya ta dakatar da Jigilar tun ranar 21 ga watan Oktobar da muke ciki, biyo bayan yadda wasu mahara suka kaiwa Jirgin hari tare da lalata shi ta hanyar saka.

Ministan ya bayyana hakan ne biyo bayan wata ziyarar gani da ido da ya kai a jiya Juma’a, yana mai cewa jirgin zai ci gaba da aiki daga yau Asabar 23 ga watan Oktoban 2021.

Haka kuma ya ƙara da cewa gwamnati ta duƙufa wajen kama waɗanda suka kai harin.

Kazalika, ya yi alƙawarin ganawa da sojoji da kuma jami’an DSS game da lamarin a birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, injiniyoyin hukumar ne suka  gyara hanyar jirgin,  kuma sun kammala aikin a kan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: