Ministan sadarwa Isa Pantami yace gudanar da ayyukan gwamnati kamar yadda ya kamata shine jigon garanbawul a Najeriya

0 72

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Ali Pantami, yace gudanar da ayyukan gwamnati kamar yadda ya kamata shine jigon garanbawul a bangaren aikin gwamnati a kasarnan.

Isa Pantami ya fadi haka a yau lokacin da yake gabatar da jawabi a taron ranar Afrika ta kasa da kasa karo na 11 da aka gudanar a Abuja, wanda kasar Slovenia ta shirya.

Yace gwamnatin da ta bayar da muhimmanci kan ‘yan kasa tana amfani da sabbin hanyoyin azurta ‘yan kasa.

Isa Pantami yayi bayanin wasu daga cikin hanyoyin da gwamnatin tarayya ke amfani da su wajen dabbaka aikin gwamnatin da zai fifita ‘yan kasa ta hanyar amfani da fasaha.

Ministan ya kuma sanar da cewa ana cigaba da kokarin fadada hanyoyin gudanar da aikin gwamnati da cin moriyarsa ga jama’a.

Ya yabawa kokarin da kasar Slovenia ta yi musamman a bangaren fasaha, inda ya roki ta hada kai da kasashen Afrika.

Leave a Reply

%d bloggers like this: