Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin kasa, inda ya ce ana bukatar Naira Biliyan 3 domin farfado da Jirgin Kasar Abuja zuwa Kaduna.

Harin da yan ta’addar suka kai a ranar Litinin ya yi sanadiyar mutawar mutum 8 akalla.

Manema Labarai sun rawaito cewa Rotimi Amaechi ya ce sai da ya bukaci a kawo kayan aikin tsaro na zamani domin a magance aukuwar wannan ta’adin.

Mista Amaechi wanda ya yi magana da manema labarai cike da bacin rai, yana mai cewa gwamnati za ta iya magance abin da ya wakana.

A cewar babban Ministan sufurin kasar, da a ce wasu ba su hana a fitar da Naira biliyan 3 wajen sayen na’urori da kayan aiki ba, da duk wannan ba ta faru ba.

Ministan ya ce kayan aikin za su taimaka wajen tsare jirgin kasan a duk wasu wurare masu hadari.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: