Ministar kudi da kasafi Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya na aro kudin da aka gano, domin aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin bana.

Ta bayyana haka ne a lokacin da ta gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai ta tarayya da ke bincike a kan kudin da aka gano, a ranar Alhamis, tare da Babban Ma’aji na kasa Ahmed Idris.

‘Yan majalisar dai sun yi tir da cire kudin daga asusun da aka tura su, ba tare da an tura su ga asusun hadin guiwa na ajiye kudin da aka gano ba.

Shugaban kwamitin Adejoro Adeogun ya tuhumi Babban Ma’ajin na kasa, bisa zargin da ake na batan Naira Miliyan 150 daga cikin kudin.

Kwamitin ya kuma ce zai gayyaci Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele domin ya yi bayanin halin da asusun ajiyar kudin ke ciki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: