Ministocin Shugaba Buhari Sun Fara Mika Mulki Ga Manyan Sakatarorin Ma’aikatun Su

0 76

Kwanaki biyar kafin karewar wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministocisa sun fara mika mulki ga manyan sakatarori a ma’aikatun su gabanin rusa majalisar ministocin.

Wa’adin mulkin shugaba Buhari na shekaru 8, wanda ya fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zai kare a ranar litinin 29 ga watan Mayun 2023.

An fara gudanar da ayyukan rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a makonnin da suka gabata. Za a gudanar da bikin rantsar da shi ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin.

Gabanin kaddamarwar, an ruwaito cewa ministan tsaro, Bashir Magashi, ya mika ragamar aiki ga babban sakataren ma’aikatar.

Wata majiya ta ce ministan zai mika mulkin yau din nan duk da cewa har yanzu shugaba Buhari bai bayyana rusa majalisar ministocinsa ba.

An gano cewa tuni Bashir Magashi ya umurci babban sakataren ma’aikatar Ibrahim Kana da ya fara aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: