Isra’ila ta bayyana damuwa kan zaɓen Ebrahim Raisi a matsayin sabon shugaban Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila, Lior Haiat, ya ce Mista Raisi shi ne shugaban kasar Iran mafi tsaurin ra’ayi da aka taɓa zaba.

Haka kuma ya yi gargaɗin cewa shugaban zai ci gaba da inganta shirin kirkirar nukiliyar Iran.

Ministan ya yi kira ga ƙasashen duniya su bayyana damuwa game da zaɓensa a matsayin shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta Iran.

A ranar Asabar ne aka ayyana Ebrahim Raisi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen Iran, zaɓen da ake ganin an shirya shine domin shi kadai ake son ya samu nasara.

Mista Raisi mai shekara 60, shi ne aƙalin alƙalan Iran wanda ke da tsattsauran ra’ayi.

Kasar Amurka ta jima da saka masa takunkumi sannan kuma ana alaƙanta shi da hukunce-hukuncen da aka yanke wa ‘yan adawar siyasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: