Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana adadin ƴan ta’addan da dakarun sojojin Najeriya suka kashe daga watan Mayun 2023 zuwa Fabrairun 2025. Mohammed Badaru ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 13,541 tare da cafke masu laifi 17,469 a tsakanin wannan lokacin.
Ministan tsaron ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, cewar rahoton jaridar TheCable.
Mohammed Badaru ya bayyana cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka ƴan ta’adda 13,541 a sassa daban-daban na ƙasar nan Ministan ya nuna cewa an ceto mutane masu yawa da aka sace, yayin da dubunnan ƴan ta’adda suka ajiye makamansu.