

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin koshin lafiya duk da cewa wasu daga cikin mukarrabansa sun kamu da cutar corona.
Mista Adesina ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin na Channels.
Adesina ya ce hadiman shugaban kasa da suka killace kan su bayan kamuwa da corona, ya nuna cewa sun kasance mutane ne kamar kowa.
Jaridar Premium Times a karshen mako ta bayyana sunayen wadanda suka kamu da cutar sun hada da Mista Yusuf Dodo; babban Jami’in tsaron Lafiyar shugaban kasa, da Malam Aliyu Musa, da kuma Mallam Garba Shehu.
A wani labarin kuma, Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Mista Chris Ngige, ya ce bai dace likitoci su ke tafiya yajin aikin ba.
Ya yi wannan jawabi ne a Abuja a wajen rantsar da wasu dalibai shida da suka kammala karatun likitanci a Jami’ar Abuja.
Ya kuma bukaci sabbin likitocin da su kauracewa shiga yajin aikin da likitoci ke yi a kasarnan.