Labarai

Mun amince mu goyi bayan mutumin da shugaba Buhari zai tsayar a matsayin wanda zai yiwa jam’iyar APC takara – Yahaya Bello

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya ce dukkanin yan Takarar shugaban Kasa na Jam’iyar APC sun amince su goyi bayan mutumin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zai tsayar a matsayin wanda zai yi Jam’iyar APC Takara.

A ranar Asabar ne Shugaba Buhari, ya gana da yan takarar shugaban kas ana Jam’iyar a fadar sa da ke Abuja.

A lokacin ganawar shugaba Buhari ya umarci yan takarkarun su fito da Dan Takara guda 1 kwakkwara, wanda zai zama na sasanto.

Gwamnan Kogi ya ce zai amince da duk mutumin da Shugaba Buhari ya bayyana a matsayin zabin sa.

Haka kuma ya ce matsayar Gwamnonin Jam’iyar APC 11 na Goyan bayan dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu, ba suyi shawara da shi ba. Inda ya bayyana goyan bayan a matsayin ra’ayin kashin kai.

A cewarsa, hakan tamkar wani yunkuri ne na raba kan kasa ta fuskar yare da yanki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: