Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da nadin Usman Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban ma’aikatan jihar.

Har ya zuwa lokacin da aka nada shi, Usman Bala Muhammad, shi ne babban sakatare a ma’aikatar yada labarai ta jihar.

Haka kuma an nada sabbin manyan sakatarori da suka hada da Muhammad Bello Shehu da Magaji Lawan da Bilyaminu Gambo Zubairu da Mairo Audi Dambatta.

A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta dakatar da gudanar da tashe, wanda aka saba farawa daga ranar 10 ga watan Ramadan mai alfarma.

Rundunar ‘yansanda ta ce an dakatar da al’adar ta bana saboda dalilai na tsaro.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: