Akalla mutane 10 ne aka ruwaito sun mutu yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti bayan sun sha shayin da ake zargin an hada da zakami a wani bikin aure a Kano.
Lamarin ya faru ne a unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.
Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, Sanusi Yahaya, wanda kuma dan uwa ne ga amaryar, ya ce ana zargin an hada shayin da wasu magunguna daban-daban bayan zakamin.
Ya ce dabi’ar matasan yankin musamman masu shaye-shayen miyagun kwayoyi suna dafa shayi a lokacin bukukuwa kuma suna fakewa da shayin domin shan kwayoyi.
An kasa samun damar jin ta bakin angon domin sanin yadda lamarin ya faru kasancewar ya gudu tare da wasu.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce har yanzu rundunar ‘yan sandar jihar da ofishin ‘yan sanda na yankin ba su samu rahoton faruwar lamarin ba.