Mutane 32 aka ruwaito sun mutu a wasu hare -hare guda biyu da aka kai jihar Sokoto

0 51

Akalla mutane 32 aka ruwaito sun mutu a wasu hare -hare guda biyu da aka kai a kananan hukumomin Gwadabawa da Sabon Birni na jihar Sokoto.

Mazauna yankunan sun ba da adadin mutanen da aka kashe a hare-haren yayin da gwamnatin jihar ta tabbatar da hare-haren amma ba ta yi magana kan adadin wadanda aka kashe ba.

Mazauna yankin sun ce mummunan lamarin ya fara ne a ranar Laraba lokacin da mambobin wata kungiyar ‘yan banga ta kashe akalla Fulani 12 a Kasuwar Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa.

Bayan faruwar lamarin, wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a ranar Juma’a sun kai harin ramuwar gayya a kasuwar Ungwan Mai Lalle da ke karamar hukumar Sabon Birni, inda suka kashe mutane sama da 20 tare da jikkata wasu da dama.

Gwamnatin jihar ta dakatar da kasuwanni a yankunan Kananan hukumomin da abin ya shafa a wani mataki na magance ayyukan ‘yan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: