Mutane 7 Sun Mutu Wasu 17 Kuma Sun Makale Bayan Ruftawar Wani Ramin Da Ake Hakar Ma’adinai

0 65

Mutane 7 ne suka mutu yayin da wasu 17 suka makale bayan da wani rami da ake hakar ma’adinai ya rufta a gundumar Birim ta Arewa da ke yankin Gabashin kasar Ghana.
A cewar kafofin yada labaran kasar, mutane biyu ne kawai daga cikin masu hakar ma’adinan da suka makale aka ceto jiya a wajen.
Rahotanni sun ce masu hakar ma’adinai na yankin da ke jagorantar aikin ceto sun hana ‘yan jarida daukar hotunan lamarin inda suka kore su.
Har yanzu dai hukumomi ba su ce uffan ba kan lamarin.
Ana zargin ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a yawancin sassan kasar ne ya haddasa ruftawar ramin.
Ana ci gaba da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kasar Ghana duk da tsaurara matakan murkushe hakan daga gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: