Mutane 7 sun mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da wasu ‘yan bindiga suka auka musu a jihar Adamawa

0 48

Mutane bakwai sun mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da wasu ‘yan bindiga suka aukawa unguwar Negga a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa.

An ruwaito cewa yan bindigar dauke da makamai ne suka shiga garin da misalin ƙarfe 11 na dare inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Unguwar Negga dai na kan iyakar jihar Adamawa da Taraba ne kuma ta fuskanci hare-hare da dama a baya-bayan nan.

Majalisar dokokin jihar ta yi tir da harin kuma ta bukaci jami’an tsaro su gaggauta kama ‘yan bindigar.

Mataimakin kakakin majalisar ya tabbatar da harin da kuma mutuwar mutanen bakwai. Haka kuma ya tabbatar da mutum bakwai sun jikkata.

Ya bukaci jami’an sojoji a yankin da su tsare mutane daga wadannan hare-hare daga wadanda ake zargin makiyaya ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: