Mutane 75 da suka gamu da iftila’in cutar kwalara sun samu tallafi a ƙaramar hukumar Malam Madori

0 182

Kimanin mutane 75 ne wanda suka gamu da iftila’in Cutar Kwalara, suka samu tallafin kayayyakin tsaftar muhalli wanda suka hada da ruwa mai tsafta da Jarkokin Omo domin tsafta a wasu garuruwa da suke karkashin Karamar hukumar Malam Madori daga hannun Kungiyar Save the Children International.

Jami’in Lura da Ayyukan Kungiyar na Jihar Jigawa Dr Adamu Isah, shine ya bayyana hakan ga Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar Alhaji Musa Muhammad, inda ya ce kayayyakin sun hada da Sabulan tsafta 75 da Jarkokin ruwa 75 da Jarkokin Sinadarin Omo 75 da kuma Sinadaran tsaftar ruwa 150.

Sauran kayayyakin da Kungiyar ta raba sun hada da Katan 10 na Izal da Katan 10 na Sanadarin Jink da Na’urar fisa 2 da sauran su.

A cewarsa, an raba kayayyakin ne ga mutanen da cutar Kwalara ta shafa a garin Shirinya da Kofar Fada da kuma unguwar Sabon Gari.

A jawabinsa, Hakimin Malam Madori Dokajen Hadejia Alhaji Muhammad Saleh Kuliya, ya bukaci wadanda suka ci gajiyar samun kayayyakin suyi amfani dashi ta hanya mai kyau.

Da yake karbar Kayan, Shugaban Sashen Lafiya a Matakin Farko na Karamar Hukumar Malam Madori, Alhaji Hamza Bello, ya bukaci Mazauna yankin suyi amfani da abubuwan da aka basu domin yin feshin a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: