Mutane Da Dama Ne Suka Mutu A Turmutsutsi Wajen Rabon Tallafin Watan Ramadan A Kasar Yemen

0 104

Mutane da dama ne suka mutu a kasar Yemen, biyo bayan wani turmutsutsi a wata makaranta da ake raba tallafin watan Ramadan.

Akalla mutane 78 ne suka mutu a Sanaa babban birnin kasar Yemen, inda daruruwan mutane suka yi cincirindo a cikin makarantar domin karbar gudunmawar ta wata mai tsarki.

Hukumomin Houthi dake mulkin garin sun ce an tsare wadanda ke da hannu a harin, amma shaidu sun ce mayakan kungiyar ‘yan tawayen da suka shafe shekaru suna iko da birnin sun haifar da firgici ta hanyar harbi a sama a matsayin wani yunkuri na shawo kan jama’a.

Faye-fayen bidiyo sun nuna yanayin da ake ciki mara kyan gani a wajen makarantar dake yankin Bab al-Yemen na birnin Sanaa.

Jami’ai a babban birnin kasar sun ce akalla mutane 78 ne suka mutu, wasu mutane da dama kuma sun jikkata, ciki har da wasu 13 wadanda a halin yanzu suke cikin mawuyacin hali. Daruruwan mutane ne suka yi dafifi a makarantar domin karbar gudunmawar kimanin dala 9, kwatankwacin naira dubu 6 ga kowane mutum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: