Mutane sama da dubu 90 ne suka kamu da cutar kwalara a Najeriya

0 78

Akalla mutane sama da dubu 90 ne suka kamu da cutar kwalara a kasarnan a bana, kamar yadda wata sanarwa da kungiyar likitocin ta Médecins Sans Frontière ta fitar a yau.

Sanarwar wacce ta samu sa hannun hadin gwiwar jami’an yada labarai biyu, Hussein Amri da Abdulkareem Yakubu, ta ce yayin da kusan daukacin Jihohin 36 suka samu rahoton bullar cutar kwalara a shekarar 2021, mafi yawan mutane sun kamu ne a jihohi shida na arewacin kasarnan wato Bauchi, Kano, Jigawa, Zamfara, Sokoto da Katsina.

Tawagogign agajin gaggawar kungiyar na aiki tare da ma’aikatar lafiya ta tarayya domin kokarin ganin an shawo kan barkewar cutar kwalara, tare da bude cibiyoyin kula da cutar kwalara guda 6 a fadin yankin tare da kula da marasa lafiya sama da dubu 20 zuwa yanzu.

Sanarwar ta ce, a yankuna da dama, rashin tsaro na haifar da kalubale; a jihar Zamfara, majinyata da dama na zuwa cikin wani hali mai tsanani, sakamakon jinkirin neman magani saboda fargabar fuskantar tashin hankali ko hadari a kan tituna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: