Mutane shida ne sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru a jihar Bauchi

0 74

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a jihar Bauchi Yusuf Abdullahi ya ce akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya faru jiya a Bauchi.

Abdullahi wanda ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, yau a Bauchi, ya ce wasu mutane 15 sun samu munanan raunuka sakamakon hatsarin.

Ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata motar bas Toyota ta Kano Line a kauyen Kwanan Digiza, kan hanyar Jama’are zuwa Azare da misalin karfe 11 da rabi na safe.

Kwamandan hukumar, wanda ya bayyana cewa gudun da ya wuce hankali ne musabbabin hatsarin, ya ce mutane 21 ne hatsarin ya rutsa da su, wadanda suka hada da maza hudu, mata 14, yaro namiji daya da yara mata biyu.

Ya kuma bayyana cewa an kai wadanda suka jikkata da kuma gawarwakin zuwa babban asibitin Jama’are a jihar ta Bauchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: