Mutum 21 sun rasa rayukansu bayan da dusar ƙankara ta rutsa da su a kasar Pakistan

0 133

Aƙalla mutune 21 ne suka rasa rayukansu bayan da dusar ƙankara mai yawa ta rutsa da su, yayin da suke ƙoƙarin zuwa gidajen su a arewacin kasar Pakistan.

Kimanin motoci 1,000 ne suka maƙale yayin da mutanen – wadanda masu yawon bude idanu ne.

Suke rububin isa wani wurin da ruwa ke kwarara daga saman dutse a garin Murree.

Wani jami’ain dan sanda da matarsa da ƴaƴansu 6, tare da wasu mutanen gida 2 suna cikin wadanda suka halaka, kamar yadda masu ceto na yankin suka sanar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Sheikh Rashid ya ce tashin hankalin ya biyo bayan cunkoson motocin matafiya da aka samu ne a yankin da ke arewa da birnin Islamabad.

Leave a Reply

%d bloggers like this: