Mutum 27 sun rasu bayan tashin gobara a wani asibitin kula da masu matsalar ƙwaƙwalwa a ƙasar Japan

0 81

Akalla mutum 27 sun rasu bayan tashin gobara a wani asibitin kula da masu matsalar kwakwalwa a birnin Osaka na kasar Japan.

Hukumomin kasar sun fara gudanar da bincike kan gobarar data tashi yau juma’a.

Dab da wayewar gari ne dai wutar ta fara ci a hawa na hudu a wani ginin asibitin.

Kafofin yada labaran kasar Japan sun nuna yadda bangaren ginin da ya kama da wuta ya kone kurmus a gobarar da suka ce mutum 27 sun mutu kawo yanzu.

Kawo yanzu dai ’yan sanda ba su tabbatar da adadin mamatan da kafar yada labaran kasar, NHK, ta sanar ba.

Tun da farko dai hukumar kashe gobara ta kasar Japan tace ana fargabar lamarin ya ritsa da rayukan mutum 27.

Sai dai a kasar Japan, likitoci ne kadai ke sanar da mutuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: