Mutum 50 ne aka kashe tare da kone gidaje 254 cikin wata 1 a jihar Kaduna

0 105

A kalla mutane 50 ne aka kashe, tare da Kone Gidaje 254 cikin wata 1, biyo bayan hare-haren da ake kaddamarwa a Masarautar Atyap ta karamar hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Shugaban Masarautar Mista Dominic Yahaya, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce an aiwatar da kisan ne a tsakanin watan Agusta zuwa Satumba.

Haka kuma gwamnatin JIhar da kuma Jami’an tsaro sun tabbatar da kaiwa hare-haren a lokutan.

Mista Dominic Yahaya, ya koka kan yadda hare-haren yan bindigar yake neman tunzura Al’ummarsa fiye da kowanne lokaci.

Shugaban Masarautar ya ce hare-haren ya tirsasawa mutane da dama barin garuruwan su, da kuma Gonakan su.

Kazalika, ya ce kimanin mutane dubu 15,000 ne suka kauracewa muhallansu a Masarautar tare da samun mafaka a sansanonin yan gudun hijira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: