Najeriya ce ke da mafi yawan yara masu cutar tamowa a kasar Afrika

544

Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (Unicef) ya bayyana cewa Najeriya ce ke da mafi yawan yara masu fama da matsanancin ƙarancin abincin masu gina jiki a nahiyar Afirka.

A cewar sanarwar da asusun ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Talata, daga cikin yara 10 da ke fama da wannan matsala biyu ne kawai ke samun magani.

Asusun ya bayyana cewa kimanin yara miliyan biyu ne a Najeriya ke fama da mmatsalar ta tamowa, inda hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan yaran da ba su girma yadda ya kamata kuma ta biyu a duniya, da kashi 32 cikin 100 na yara ‘yan ƙasa da shekara biyar.

Hakazalika, Unicef ya ce kashi 7 cikin 100 na mata masu haihuwa a Najeriya na fama da matsanancin ƙarancin abinci.

Asusun ya nuna damuwa kan yadda ƙarancin abinci ke haddasa kashi 45 cikin 100 na mace-macen yara ‘yan ƙasa da shekara biyar tare da barazana ga lafiyar jama’a da tattalin arziki.

Comments are closed.

hitta mer om recensioner