Najeriya a yau ta shiga jerin kasashen da aka samu bullar kwayar cutar corona nau’in Omicron.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Darakta Janar, Ifedayo Adetifa ya sanya wa hannu a safiyar yau.

Hukumar ta ce an gano nau’in a jikin mutane biyu. Daga baya ya fayyace cewa an tabbatar da nau’in cutar jikin mutane uku.

Wannan na zuwa ne bayan kasar Kanada ta ce ta gano nau’in cutar a jikin matafiya biyu da suka fito daga Najeriya.

A halin da ake ciki, gwamnatin kasar Kanada ta haramtawa ‘yan Najeriya shiga kasarta, a yunkurinta na dakile yaduwar cutar corona nau’in Omicron.

Kasar da ke samun kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan da sanyin safiyar yau.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: