Najeriya ta tabbatar da kammala biyan bashin dala biliyan 3.4 da ta karɓa a lokacin annobar COVID-19
Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya tabbatar da cewa Najeriya ta kammala biyan bashin dala biliyan 3.4 da ta karɓa a lokacin annobar COVID-19 a ƙarƙashin tsarin Rapid Financing Instrument (RFI).
Sai dai duk da wannan tabbaci, har yanzu Najeriya na da ragowar bashi da ya kai kimanin dala miliyan 30 — daidai da naira biliyan 48.2 — wanda za a rika biya kowace shekara na tsawon shekaru huɗu, a matsayin kuɗin amfani da lamunin na musamman (Special Drawing Rights – SDR). Wannan adadi zai kai sama da naira biliyan 190 gaba ɗaya.
SDR dai wata kadara ce da IMF ke ƙirƙira domin ƙarfafa ajiyar ƙasashen duniya, inda membobin ƙungiyar ke amfani da su a matsayin kuɗin ajiyar ƙetare, kuma za su iya musanya su da kudaden wasu ƙasashe mambobi.
Sai dai sanarwar biyan bashin da aka bayyana a hukumance daga fadar shugaban ƙasa, ta haifar da ruɗani da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya, kasancewar ana ci gaba da sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa yawaitar bashin cikin gida da na waje.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Otega Ogra, ya wallafa sakon farin ciki a shafinsa na X inda ya sanar da fitar Najeriya daga jerin ƙasashen da IMF ke bin bashi. A cewar rahoton jaridar Daily Trust, wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake sukar yadda bashin cikin gida da na ƙetare ya karu, wanda ya kai fiye da naira tiriliyan 144.67 zuwa ƙarshen watan Disamba 2024, a cewar Hukumar Kula da Bashi ta Ƙasa (DMO).