Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 3 a yayin gobara sama da 2000

0 64

Najeriya ta yi asarar Naira Tiriliyan 3 a yayin gobara 2,845 data barke a shekarar 2021, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola.

Mista Aregbesola ya bayyana hakan ne a jiya Larabar yayin da yake yiwa sabbin mataimakain Kwanturola-Janar, na Hukumar Kashe Gobara ta kasa.

Ministan ya kuma ce hukumar ta ceci kadarorin da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 18.9, da rayuka 587 tare da ceto mutane 260 daga gobarar da ta tashi.

Ya ce, a shekarar 2021, hakumar ta amsa kiraye-kirayen kai dauki 2,845.

Ya ci gaba da cewa, a dunkule, hannun jarin hakumar ya karu matuka, domin hukumar ta bayar da gudunmawa sosai ga tsaron kasa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Aregbesola ya bayyana cewa dalilin da ya sa aka samu irin wannan nasarar shi ne, a tsakanin shekarar 2015 zuwa yanzu, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi karin kudi a hidimar idan aka kwatanta da tun da aka kafa ta a shekarar 1901.

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da shirin gyara kasafin kudin 2022 biyo bayan gyare-gyaren farko da majalisar dokokin kasar ta yi kan kudirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a shekarar 2021.

Leave a Reply

%d bloggers like this: