Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana tafiyar dimokiraɗiyyar ƙasar a matsayin ginshiƙin zaman lafiya a yankin yammacin Afirka.
A wata sanarwa da ya fitar don tunawa da ranar Dimokiraɗiyya, ya ce jajircewar Najeriya wajen gudanar da sahihan zaɓe, haɗa al’umma da bin doka da oda ya bambanta ta da ƙasashen makwabta da ke fuskantar juyin mulki da rushewar dimokiraɗiyya.
Ya tabbatar da cewa Najeriya na ci gaba da goyon bayan diplomassiya da aikin wanzar da zaman lafiya karkashin kungiyar ECOWAS, yana mai gargadin cewa nasarar tsarin mulki a Najeriya na da tasiri kai tsaye ga zaman lafiya a yankin.
Ya kara da cewa gyare-gyaren Shugaba Bola Tinubu na daga cikin matakan da za su karfafa dimokiraɗiyya da habaka ci gaba na tsawon lokaci.