Najeriya zata fara kwaso ‘yan ƙasarta sama da 15,000 da suka maƙale a wasu ƙasashe

0 52

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar yadda zata kwaso ‘yan ƙasarta sama da 15,000 da suka makale a kasashen Kamaru, Nijar, Chadi da ma wasu ƙasashenGwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar yadda zata kwaso ‘yan ƙasarta sama da 15,000 da suka makale a kasashen Kamaru, Nijar, Chadi da ma wasu ƙasashenGwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar yadda zata kwaso ‘yan ƙasarta sama da 15,000 da suka makale a kasashen Kamaru, Nijar, Chadi da ma wasu ƙasashen

.

Kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira da baƙin haure ta ƙasar, Alhaji Tijani Ahmed ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Ahmed ya bayyana cewa aƙalla mutane miliyan shida ne suka rasa matsugunansu a Najeriya, yayin da dubban ‘yan gudun hijira ke zaune a wasu yankuna da ke wajen ƙasar.

“Muna da ‘yan Najeriya 15,000 da ke son komawa gida bisa raɗin kansu, haka nan muna da ‘yan ƙasashen waje kusan 100,000 da ke zaune a ƙasarmu a matsayin ‘yan gudun hijira,” in ji Tijani.

Yayin da yake nanata ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa gida cikin ƙoshin lafiya, Ahmed ya kuma yabawa gwamnati, bisa irin gudun mowar da take bawa hukumar da kuma ma’aikatar jin ƙai wajen tunkarar ƙalubalen da ke gabansu.

Leave a Reply