Nan Bada Dadewa Ba Za’a Kawo Karshen Karancin Wutar Lantarki A Najeriya

0 77

Gwamnatin tarayya ta ce gadar Neja ta biyu da za a fara amfani da ita a ranar 20 ga watan Mayu, yanzu haka an shirya bude ta.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.

Karamin ministan wutar lantarki, Jeddy Agba, ya ce majalisar ta amince da bayar da kwangilar sayen wasu na’urori 25 na katse wutar lantarki da wasu na’u’rorin 120 masu daidaita wutar lantarki domin amfanin kamfani watsa wutar lantarki na kasa TCN.

Jeddy Agba ya ce kudin kwangilar ya kai kimanin naira miliyan 140.

Ya ce majalisar ta kuma amince da tashin farashin kwangilar gina tashar wutar lantarki ta Dukanbo Shonga mai karfin KV 132 a jihar Kwara.

Jeddy Agba ya bayar da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a kawo karshen karancin wutar lantarkin da ake fama da ita a sassan kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: