Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama miyagun ƙwayoyi da kimarsu ta kai fiye da naira biliyan 2.6 a nan jihar Jigawa.
Kwamandan hukumar na jiha, Musa Maina, ya ce an gudanar da aikin sirri tsawon kwanaki uku a Jigawa da Kano kafin a yi nasarar kama mutanen uku da motoci biyu dake ɗauke da ƙwayoyin.
Kayayyakin da aka kama sun haɗa da Tramadol da Pregabalin.
Ya ce wannan ita ce babbar nasara da hukumar ta samu a jihar wajen yaƙi da safarar ƙwayoyi.