NEMA ta tarbi ƴan Najeriya 147 da aka dawo da su daga Nijar

0 189

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA), reshen jihar Kano ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 147 da aka dawo da su daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce mutanen sun sauka ne a filin Jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:48 na rana a ranar 16 ga Yunin 2025.

Hukumar kula da ƙaura ta Duniya (IOM) ta ce tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi masu kula da harkokin ‘yan ci-rani suka jagoranci dawo da su gida.

NEMA ta ce, waɗanda aka dawo da su sun ƙunshi maza 143, da mace guda da kuma ƙananan yara uku.

An kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka dawo da su na fama da rashin lafiya, kuma ya samu kulawar gaggawa daga ƙungiyar agaji ta Red Cross da ke wajen bayar da taimako a wurin.

Leave a Reply