Netanyahu ya shaida wa Amurka cewa yana adawa da kafa ƙasar Falasɗinawa

0 82

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce ya shaida wa Amurka cewa yana adawa da kafa ƙasar Falasɗinawa da zarar an kawo ƙarshen rikicin Gaza.

A wani taron manema labarai, Mista Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a Gaza har sai an samu cikakkiyar nasara a cewar sa, lalata Hamas da kuma ƙwato sauran mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su, ya kara da cewa hakan zai iya daukar  watanni masu yawa.

Kimanin Falasdinawa dubu 25 ne aka kashe a Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas, kuma kashi 85 cikin 100 na al’ummar Zirin sun rasa matsugunansu, Isra’ila na fuskantar matsin lamba na ganin ta tsagaita kai hare-hare tare da shiga tattaunawa mai ma’ana domin kawo ƙarshen yaƙin.

Kawayen Isra’ila, ciki har da Amurka, da kuma da yawa daga cikin abokan hamayyarta, sun buƙaci a farfado da matsayar kafa ƙasashe biyu, inda za a samu ƙasar Falasdinawa wadda za ta yi maƙwabtaka da Isra’ila. Fatan da ake da shi a ɓangarori da dama shi ne rikicin da ake fama da shi zai tilasta wa ɓangarorin da ke fada da juna su koma tattaunawa ta diflomasiyya, a matsayin hanya daya tilo da za ta iya magance tashe-tashen hankula da aka daɗe ana fama da su. Amma daga kalaman Netanyahu, aniyarsa ta bayyana akasin haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: