Ni ne wanda zai iya magance matsalar ta’addanci da rashin tsaro a Najeriya idan aka zabe ni a 2023

0 90

daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa zai yaki ta’addanci da rashin tsaro a kasar nan idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.

Ya bayyana haka ne jiya a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a babban taronta na musamman da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a dandalin Eagle Square dake Abuja.

Bola Tinubu ya yabawa sauran ’yan takara 23 da za su fafata a zaben bisa gudanar da abin da ya bayyana a matsayin yakin neman zabe mai tsafta, inda ya ce a karshe hakan zai karawa APC karfi.

Ya bayyana kansa a matsayin mai hada kan al’umma kuma ake bukata bisa la’akari da halin da kasarnan ke ciki.

Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya ce yana da gogewa, tarihin nasarori da kuma iya tafiyar da shugabanci nagari idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasarnan.

Bola Tinubu ya kara da cewa gyara da ci gaba na gaskiya ba wai a kwaikwayi wasu ba ne, sai dai mu gano damarmakinmu a matsayin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: